Yahaya Bello: Sanatan PDP Ta Yabawa EFCC Tare da Shawartar Tsohon Gwamnan
- Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yabawa hukumar EFCC kan ƙoƙarin cafke Yahaya Bello
- Natasha ta soki tsohon gwamnan na Kogi kan ƙin amincewa da yunƙurin hukumar yaki da cin hanci da rashawan na tsare shi
- Sanatan ta yabawa shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede bisa jajircewarsa wajen kawar da masu cin hanci da rashawa a ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta tsakiya, ta caccaki tsohon gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi kan gujewa shari’a.
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta ayyana tsohon gwamnan matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bayan ya ƙi amsa gayyatar da ta yi masa.
Yahaya Bello ya yi martani kan zargin biyan kudin makarantar 'ya'yansa daga asusun Kogi
Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan ne domin bayyana yadda wasu makuɗan kuɗaɗe da suka kai Naira biliyan 80.2 suka ɓace daga asusun gwamnatin jihar a lokacin da yake mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Natasha ta yabawa yadda hukumar EFCC ta yi tsayin daka duk kuwa da matsin lambar da take fuskanta, cewar rahoton jaridar Leadership.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Yahaya Bello ya bayyana cewa tsoron cafke shi ne ya sanya ya ƙi fitowa domin ya bayyana a gaban kotu.
Wace shawara ta ba Yahaya Bello?
"Na yi mamakin jin cewa Yahaya Bello ya ƙi amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa, duk da cewa ya taɓa rike muƙamin tsohon babban jami'in tsaron jihar Kogi."A matsayinsa na tsohon gwamna, ya kamata ya fahimci muhimmancin mutunta dokoki da tsarin mulkin Najeriya.""Saboda haka ina shawartarsa ya amsa gayyatar domin ya wanke kansa yayin da yake da sauran dama."Ana cikin nemansa Yahaya Bello ya kalubalanci hukumar EFCC
- Natasha Akpoti
Ta kuma jaddada cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka, duk kuwa da irin muƙamin da ya taɓa riƙewa a baya.
Ta shawarci EFCC da kada ta ci amanar jama’a, ta kuma ci gaba da bincike har zuwa ƙarshensa, rahoton jaridar Businessday ya tabbatar.
Barazanar EFCC ga Yahaya Bello
A wani labarin kuma kun ji cewa hukumar EFCC ta yi barazanar yin amfani da sojoji wajen kamo tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, daga inda yake ɓoye.
Hukumar ya ƙi da cin hanci da rashawan ta yi wannan barazanar ne bayan tsohon gwamnan ya ƙi yarda jami'an hukumar su cafke shi a gidansa.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbYZ5fZVmsJqgka6ubq7EpaOoZaOWu6LAwKdkqZygYsGiediamZqvkWKyp6%2FCZquaqpVisaJ50qGYsJmiqa6zedOspqGnnmK0uK3Mp5inZw%3D%3D